Isa ga babban shafi
Chadi

'Yan sandan Chadi sun tarwatsa masu zanga-zanga da barkonon tsohuwa

‘Yan sanda a Chadi sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa daruruwan masu zanga zanga da suka fito don caccakar sojojin da suka dare madafun iko bayan mutuwar shugaba Idriss Deby Itno.

Ko a watan Satumba sai gamayyar jami'iyyun siyasa suka gudanar da zanga-zanga.
Ko a watan Satumba sai gamayyar jami'iyyun siyasa suka gudanar da zanga-zanga. Djimet WICHE AFP
Talla

Gamayyar jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da  ake kira Wakit Tamma ce ta shirya wannan gangami don nuna rashin amincewa da gwamnatin wucin gadin kasar da sojoji ke jagoranta.

Gwamnatin sojin Chadin na karkashin jagorancin Mahamat Idriss Deby Itno, da ga shugaban kasar da ya mutu a sanadiyyar yaki da ‘yan tawayen arewacin kasar a watan Afrilu, bayan ya shafe sama da shekaru 30 yana mulkin kasar.

Deby karami ya sha alwashin gudanar da zabe  mai tsafta a kasar, bayan wani shirin sasantawa na watani 18.

Da izinin hukumomin Chadiin aka fito zanga zangar, sai dai masu zanga zanga sun dau wata hanya da ba ta cikin wadanda aka amince su bi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.