Isa ga babban shafi
Chadi

Sojojin Chadi sun kafa majalisar dokokin rikon kwarya

Shugaban gwamnatin sojan Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana mambobi 93 na sabuwar majalisar rikon kwaryar kasar, watanni biyar bayan ayyana kansa a matsayin shugaba, sakamakon rasuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno.

Mahamat Idriss Deby Itno, shugaban kasar Chadi.
Mahamat Idriss Deby Itno, shugaban kasar Chadi. AFP - BRAHIM ADJI
Talla

Idan za a tuna a ranar 20 ga Afrilu, Mahamat Idriss Deby ya rusa majalisar Chadi tare da yin alkawarin shirya zabe cikin watanni 18, bayan ayyana kansa a matsayin sabon shugaba.

Akwai dai masu adawa da tsohon shugaba Deby cikin membobin majalisar dokokin rikon kwaryar ta Chadi, sai dai babu mamba ko guda daga cikin kungiyar ‘yan adawa ta Wakit Tamma, ko kuma daga kungiyoyin farar hula da suka yi tir da darewa shugabancin Chadi da karamin Deby ya yi.

Ranar 11 ga watan Mayu, gwamnatin sojin Chadi ta nada tsohon firaministan kasar Albert Pahimi Padacke, kan tsohon mukamin nasa amma na rikon kwarya.

Pahimi Padacke dai shi ne Firaminista na karshe a karkashin tsohon shugaban Chadi marigayi Idriss Deby Itno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.