Isa ga babban shafi
Chadi

Rikicin Makiyaya da Manoma ya hallaka mutane 27 a Chadi

Wasu bayanai daga Chadi na nuna yadda mutane akalla 27 suka rasa rayukansu sanadiyyar wani rikici da ya barke tsakanin Makiyaya da Manoma a gabashin kasar.

Wasu Makiyaya a Chadi.
Wasu Makiyaya a Chadi. © Sayouba Traoré/RFI
Talla

Majiyoyin da ke tabbatar da rikicin sun ce tun a lahadin da ta gabata ne fadan ya barke tsakanin makiyayan da manoma a kauyukan Kidji-Mina da Tiyo mai tazarar kilomita 40 da birnin Abeche.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa, ministan shari’a na Chadi Mahamat Ahmat Alhabo ya ce rikicin na da nasaba da badakalar da ta dabaibaye sayar da wasu filaye a kauyukan biyu.

A cewarsa, sarakunan gargajiyar kauyukan biyu sun sayar da filayen kiwo da na nom aba bisa ka’ida ba, matakin da ya harzuka makiyayan da manoma wanda ya juye zuwa rikici tsakaninsu.

Ministan shari’ar wanda ke tabbatar da kisan mutane 27 a rikicin wanda ya alakanta da kama karyar shugabannin gargajiya yayin taron masu ruwa da tsaki a Abeche ya yi fatar daukar matakan dakile rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.