Isa ga babban shafi
Rwanda - Shari'a

Kotu ta samu jarumin Hotel Rwanda Rusesabagina da laifin ta'addancin

Wata kotu a Rwanda ta samu Paul Rusesabagina, da yayi fitce a fim din ‘Hotel Rwanda’ da kamfanin shirya fina finan Amurka a shekarar 2004 da laifin ta’addanci.

Paul Rusesabagina, ranar 17 ga watan Satumba 2020 yayin da ya gurfana a kaban Kotun Kigali.
Paul Rusesabagina, ranar 17 ga watan Satumba 2020 yayin da ya gurfana a kaban Kotun Kigali. - AFP/Archivos
Talla

Da take sanar da hukuncin Alkali Beatrice Mukamurenzi tace ta samu mutanen 20 dake gabanta ci harda Rusesa-bagina da laifin kasancewa cikin kungiyar ta’addanci na MRCD-FLN, da suka rika kaiwa mutane hare-hare gidajensu, ko ma tare su cikin motocin su.

Rusesabagina da Lauyansa cikin Kotu a Kigali, 20/09/21.
Rusesabagina da Lauyansa cikin Kotu a Kigali, 20/09/21. © Laure Boulard / RFI

Wannan shari’ar dai ta yi kaurin suna tun bayan da aka kama Rusesabagina, mai shekara 67, a bara lokacin ya isar Rwanda daga Dubai, yana mai bayyana matakin a matsayin garkuwa da shi hukumomin Rwanda suka yi.

Rusesabagina tare da rakiyar jami'an tsaro a watan Fabarerun 2021.
Rusesabagina tare da rakiyar jami'an tsaro a watan Fabarerun 2021. Simon Wohlfahrt AFP/File

Rusesabagina wanda yayi fitce a fim din Hotel Rwanda da Hollywood na Amuka ta shirya game da kisan kiyashin shekarar 1994, ya dade yana sukar shugaban kasa Paul Kagame, wanda yake bayyana shi a matsayin dan kama karya, kafin a kama shi a watan Agustan bara.

Masu gabatar da kara sun bukaci kotu ta yankewa Rusasebagina hukuncin daurin rai-da-rai, a shari’ar da ta gamu da suka daga ciki da wajen Rwanda.

Rusesabagina tare da shugaban Amurka George W. Bush a shekarar 2005, lokacin da ya samu lambar yabon shugabancin Amurka.
Rusesabagina tare da shugaban Amurka George W. Bush a shekarar 2005, lokacin da ya samu lambar yabon shugabancin Amurka. MANDEL NGAN AFP/File

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.