Isa ga babban shafi
KULA DA LAFIYA

Sudan ta Kudu zata yiwa balagaggu miliyan guda da rabi kaciya

Gwamnatin Sudan ta Kudu tace zata yiwa maza ‘yan kasar miliyan guda da rabi dake tsakanin shekaru 15 zuwa 49 kaciya a wani yunkuri na yaki da cutar HIV.

Shugaban kasa Salva Kiir
Shugaban kasa Salva Kiir REUTERS - JOK SOLOMUN
Talla

Wannan ya biyo bayan binciken da aka gudanar wanda ya nuna cewar maza sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar lokacin jima’i saboda rashin yin kaciyar.

Wata kungiyar agaji ta ‘Human Appeal Associates’ ta cimma yarjejeniya da ma’aikatar lafiyar kasar domin neman mutanen da ba’a yiwa kaciyar ba, dan ganin sun mika kan su a musu nan da shekaru 5 masu zuwa.

Rahotanni sun ce a Jihohi 3 daga cikin Jihohi 10 da ake da su a Sudan ta kudu ne kawai ake yin kaciya, yayin da sauran yankunan ke kyamar ta.

Gwamnatin kasar ta bayyana rashin yin kaciyar a matsayin babbar barazana ga harkokin kula da lafiyar kasar, musamman wajen yaki da cutar HIV.

Majalisar Dinkin Duniya tace a karshen makon da ya gabata, akalla maza 100 dake tsakanin shekara 15 zuwa 49 suka ci gajiyar wannan sabon shirin wajen gabatar da kan su a musu kaciyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.