Akalla baki 47 suka mutu a gabar ruwan Mauritania
Majalisar Dinkin Duniya tace akalla bakin haure 47 suka mutu a gabar ruwan Mauritania bayan da kwale kwalen su ya kife a ruwa.
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da kaurar baki tace kwale kwalen wanda ya bar Yankin Laayoune dake Yammacin Sahara ranar 3 ga watan Agusta na kan hanyar zuwa tsibirin Canaries mallakar kasar Spain ne lokacin da ya gamu da hadarin.
Nicolas Hochart na hukumar kula da kaurar bakin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar injin din kwale kwalen ya gamu da matsala, yayin da yayi ta yawo akan ruwa na makwanni 2 kafin jami’an tsaron dake kula da gabar ruwan Mauritania su gano shi.
Hochart yace sun yi nasarar gano mutane 7 da suka tsira da ran su.
Majalisar Dinkin Duniya ta dade tana gargadi dangane da hadarin dake tattare da irin wannan tafiya mai hadari wanda Yan Afirka keyi zuwa Turai domin samu rayuwa mai inganci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu