Shugaban Congo ya bukaci yan kasar su bayar da hadin kai wajen karbar allurar covid 19
Shugaban kasar Congo Brazzavile Denis Sassou Nguesso a yau lahadi ya yi kira ga daukacin yan kasar da su bada hadin kai na ganin kowanen su ya karbi allurar rigakafin cutar Covid 19.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya ce bayar da hadin kai zai taimaka wajen rage yawan masu kamuwa da cutar a wannan kasa inda alkaluma ke nuna cewa kusan kashi biyu daga cikin yawan al’umar ne suka karbi wannan allura yanzu haka,duk da cewa wasu mutanen na ci gaba da nuna adawar su a kai.
A watan Afrilun shekarar bana gwamnatin wannan kasa ta kaddamar da shirin yiwa yan kasar wannan allura kamar dai sauren kasashen Duniya.
A hukumance sama da mutane dubu 13.300 ne suka kamu da cutar a Congo Brazzaville yayinda 179 suka bakuci lahira.
Ko a baya a matakin yaki da wannan cuta sai da hukumomin kasar tareda yardar kamfanin Air France mallakin kasar Faransa suka cimma yarjejeniya na dakatar da duk wata zirga-zirga daga kasar zuwa waje,kazzalika daga waje zuwa cikin kasar ta Congo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu