Daya daga cikin yan takara a zaben Congo Brazzaville ya kamu da cutar Covid 19
A Congo Brazzaville akalla mutane milyan 2 da dubu dari 5 ne za su fito don kada kuri’ar su a zaben yau lahadi,daya daga cikin yan takara 6 ya kamu da cutar Coronavirus.Shugaban kasar mai ci Denis Sassou Nguesso mai shekaru 77, da ya share kusan shekaru 36 a kan karagar mulkin kasar na daga cikin masu neman wanna kujera.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka wasu daga cikin Shugabanin kungiyoyin Farraren hula tareda hadin gwiwar wasu jam’iyyun adawa na kira ga yan kasar na ganin sun kauracewa zaben na yau lahadi.
Iyalan daya daga cikin yan takara a zaben,wanda da ya bayyana kamuwa da cutar Coronavirus ,Guy Brice Parfait Colela sun sanar da cewa suna kan hanyar isa da mutumen su kasashen waje don neman magani ganin tsanatar ciwon da yake fama da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu