Isa ga babban shafi
AFIRKA-SIYASA

Baiwa Isra'ila kujera a Kungiyar AU ya kawo rarrabuwar kawuna

Baiwa kasar Isra’ila matsayin ‘Yar kallo a Kungiyar Kasashen Afirka ta AU ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen dake cikin kungiyar.

Shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat
Shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat © AFP - Ludovic Marin
Talla

Shugaban gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat ya baiwa Israila wannan matsayi abinda ya kawo karshen sama da shekaru 20 ana kin amincewa da bukatar ta na samun wannan matsayi.

Wannan ya biyo bayan zargin da ake mata na take hakkin Falasdinawa da kuma kin basu ‘yancin cin gashin kan su abinda da ake cewa yayi karo da muradun AU na ganin kowacce kasa ta samu ‘yancin walwala a duniya.

Tuni wasu daga cikin kasashen dake cikin kungiyar suka bayyana rashin amincewar su da matakin wanda suka ce ya sabawa dokokin su, yayin da wasu suka bukaci cikakken bayani akan dalilin daukar matakin ko kuma janye shi baki daya.

Alamun kungiyar kasashen Afirka ta AU
Alamun kungiyar kasashen Afirka ta AU www.au.int/

Israila ta taba samun wannan matsayin lokacin da kungiyar kasashen Afirka ke amsa sunan OAU amma daga bisani da aka sauya ta zuwa AU a shekarar 2002 sai aka janye damar.

Daga cikin kasashen da suka bayyana adawar su da baiwa Israila wannan matsayi akwai Afirka ta Kudu da Masar da Algeria da Tunisia da Djibouti da Mauritania da Comoros da kuma Libya.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Algeria ta gabatar yace rashin tintiba da kuma tattaunawa kafin daukar matsayin baiwa Israila wannan matsayin ya sabawa dokokin da akayi amfani da su wajen kafa kungiyar AU.

Shima ministan harkokin wajen Namibia yace suna adawa da matakin domin ya sabawa manufofin kungiyar ta su.

Taron shugabannin kungiyar kasashen Afirka a Addis Ababa
Taron shugabannin kungiyar kasashen Afirka a Addis Ababa Reuters/Tiksa Negeri

Ita ma kasar Afirka ta Kudu ta bayyana kaduwar ta da matakin da shugaban gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat yayi gaban kan sa wajen dauka na baiwa Israila wannan matsayi, yayin da Botswana tace batun na da girmar da ya dace ace an gudanar da taro akan sa kafin daukar matsayi.

Israila na cewar samun matsayin zama ‘yar kallon zai bata damar kulla dangantaka mai karfi da kasashen dake cikin kungiyar ta AU, wadanda tuni aka samu wasu daga cikin su da suka kulla huldar diflomasiya tare, amma kuma wasu na cewar baiwa Israila matsayin yayi karo da manufofin kungiyar na tabbatar da ‘yanci a duniya lura da matakin da kasar ke dauka akan Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.