Isa ga babban shafi
RIKICIN SUDAN TA KUDU

Kazamin fada ya barke tsakanin magoya bayan Jam'iyyar SPLA

Wani kazamin fada ya barke tsakanin magoya bayan mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar da shugabanin bangaren Jam’iyyar sa ta SPLA-IO da suka sanar da sauke shi daga jagorancin ta a karshen makon jiya.

Shugaban kasa Salva Kiir
Shugaban kasa Salva Kiir REUTERS - JOK SOLOMUN
Talla

Kakakin bangaren sojin dake goyan bayan Machar Kanar Lam Paul Gabriel yace dakarun dake goyan bayan Janar Simon Gatwech Dual sun kaddamar da hare hare a yankunan da magoya bayan mataimakin shugaban kasar suke dake Jihar Upper Nile abinda ya sa suka mayar da martani.

Jami’in yace dakarun su sunyi nasarar kashe masu rike da mukamin Manjo Janar guda 2 da wasu sojoji 27, yayin da su kuma suka rasa sojojin su guda 3.

Babu wata majiya ta daban da ta tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da bangaren Gatwech yaki amsa tambayoyi dangane da rikicin.

Mataimakin shugaban kasa Riek Machar
Mataimakin shugaban kasa Riek Machar Akuot Chol AFP/File

Kanar Gabriel ya bayyana cewar an dauki Laftanar Janar Dual da wani mai mukami irin na sa zuwa Sudan domin samun mafaka, yayin da ya bukaci magoya bayan su da su dawo gida.

Jami’in ya kuma bukaci gwamnatin Sudan da kada ta sanya hannu a cikin rikicin da kuma bukatar hana Janar Janar din komawa gida domin kaucewa tashin hankali.

Taswirar Sudan ta Kudu
Taswirar Sudan ta Kudu AFP

Bayan wani taro da shugabannin SPLA suka yi a karshen makon jiya, sun sanar da sauke Machar daga mukamin sa saboda abinda suka kira gazawar sa wajen jagoranci na gari da kuma kare muradun Jam’iyyar su.

Magoya bayan Machar sun bayyana yunkurin sauke shi a matsayin juyin mulkin da bai samu nasara ba, yayin da shi da kan sa ya zargi marasa son zaman lafiya da kitsa masa bore.

Rikicin cikin gida a Sudan ta Kudu yayi sanadiyar haifar da yakin basasar da tayi sanadiyar kashe akalla mutane 400,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.