Isa ga babban shafi
Congo Brazzaville

Shugaban Congo ya zarce kan sabon wa’adi bayan shafe shekaru 37 kan mulki

Yau juma’a aka rantsar da Denis Sassou Nguesso a sabon wa’adin shugabancin kasar Congo Brazzaville, bayan da ya yi nasara a zaben da aka yi ranar 21 ga watan jiya.

Shugaban Congo Brazaville Sassou Nguesso.
Shugaban Congo Brazaville Sassou Nguesso. © AP - Francois Mori
Talla

Shugaba Nguesso, mai shekaru 77 a duniya, ya yi rantsuwar kama aiki ne domin yin wa’adin mulki na shekaru 5, a daidai lokacin da yake daf da cika shekaru 37 a kan karagar mulkin kasar da ke yankin tsakiyar Afirka.

A jawabinsa jim kadan bayan ya yi rantsuwar, shugaba Denis ya ce zai yi iya kokarinsa domin kare gandun dajin zagayen kogin Congo da ke da matukar muhimmanci wajen kare halittu da sauran tsirrai da duniya ke matukar alfahri da su.

Magoya bayan dan takarar shugabancin kasar Congo daga bangaren 'yan adawa Guy Brice Parfait Kolelas, yayin yakin neman zabe a birnin Brazaville.
Magoya bayan dan takarar shugabancin kasar Congo daga bangaren 'yan adawa Guy Brice Parfait Kolelas, yayin yakin neman zabe a birnin Brazaville. AP - Christ Kimvidi

A game da siyasar cikin gida kuwa, shugaban ya ce zai dauki matakin ba-sani-ba-sabo a kan masu handame dukiyar kasa da kuma masu azurta kansu ta barauniyar hanya, a daidai lokacin da kungiyoyi masu zaman kansu ke zargin wasu manyan jami’an gwamnatin kasar da mallakar gidaje da kuma kaddarori a kasashen ketare.

An dai gudanar da bikin ne a gaban shugabannin wasu kasashen akalla 20, da suka hada da Angola, Burkina Faso, Burundi, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da kuma Cote d’Ivoire. Sauran sun hada da na Ghana, Guinea, Liberia, Mali, Niger, Senegal, Chadi da kuma Togo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.