Isa ga babban shafi
Congo Brazzaville - Zabe

Al'ummar Congo Brazaville na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

An fara kada kuri’a a zaben shugaban kasar Congo Brazaville a Lahadin nan, zaben da babbar jam’iyyar adawa ta kaurace wa, kana masu sharhi  na cewa an tsara shi ne ta yadda shugaba mai ci, Denis Sassou Nguesso zai kai ga nasara.

Shugaban Congo Brazaville Denis Sassou Nguesso wanda ya shafe shekaru 36 yana mulkin kasar.
Shugaban Congo Brazaville Denis Sassou Nguesso wanda ya shafe shekaru 36 yana mulkin kasar. REUTERS/Anis Mili/Files
Talla

Da karfe 6 na safe agogon GMT aka bude rumfunan zabe, inda ake sa ran rufewa da karfe 4  na yamma agogon GMT.

Fiye da mutane miliyan 2 da rabi ne suka yi rajistan kada kuri’a a wannan zabe, wanda ake kyautata zaton shugaba mai ci Nguesso mai shekaru 77, wanda ya shafe shekaru 36 yana mulkin kasar  zai samu galaba a kan ‘yan takara 6 da ke hamayya da shi.

Dan takaran da ke kan gaba a cikin masu hamayya da shugaba Nguesso shi ne Guy-Price Parfait Kolelas, wanda aka kwantar a gadon asibiti a ranar Asabar.

Tawagar yakin neman zaben Kolelas ba ta bayyana takamammen abin da ke damunsa ba, amma wani daga cikin iyalansa ya ce gwaji ya tabbatar dan shekara 60 din ya harbu da cutar Coronavirus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.