Isa ga babban shafi
Congo Brazzaville

Dan takaran shugaban kasar Congo ya mutu

Dan takara na jam’iyyar adawa a Jamhuriyar Congo Guy-Brice Parfait Kolelas ya mutu bayan fama da cutar coronavirus a daidai lokacin da ake kan hanyar kai shi Faransa domin yi masa magani kamar yadda darektan yakin neman zabensa ya bayyana.

Marigayi Guy-Brice Parfait Kolélas ya mutu ne a cikin jirgin sama
Marigayi Guy-Brice Parfait Kolélas ya mutu ne a cikin jirgin sama AFP - MARCO LONGARI
Talla

Rasuwarsa na zuwa ne kwana guda da zaben shugabancin kasar, inda ya kasance babban dan takara daga bangaren jam’iyyar adawa.

Kolelas ya mutu ne a cikin jirgin saman da ya dauko shi daga Brazzaville a yammacin jiya Lahadi yana da shekaru 66 a duniya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwaji ya nuna cewa yana dauke da cutar coronavirus, inda har ya gaza gudanar da taron yakin neman zabensa  na karshe a birnin Brazaville.

Marigayin ya wallafa hoton bidiyonsa  daga gadon jinyarsa, inda ya shaida wa magoya bayansa cewa, yana yaki da mutuwa.

Ana kallon Kolelas a matsayin babban mai kalubalantar shugaban kasar mai ci Denis Sassou Nguesso wanda ake sa ran zai lashe zaben na ranar Lahadi.

Kodayake  ‘yan adawa sun kaurace wa zaben, yayin da aka katse hanyoyin sadarwar intanet. 

Masharhanta sun bayyana shakkunsu kan sahihancin zaben ganin  yadda alamu suka nuna cewa, an bai wa shugaba Nguesso fifiko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.