Isa ga babban shafi
Somaliya - Al-Shebaab

Al-Shabaab ta kai hari wasu sansanonin sojin Somaliya har biyu lokaci guda

Mayakan kungiyar Al-Shabaab masu kaifin kishin Islama sun kai hari kan wasu muhimman sansanonin soja biyu a Somalia yau Asabar, inda suka tayar da bama-bamai a cikin motoci a wuraren biyu kafin su shiga gwabza kazamin fada, acewar wani jami’in soja da kuma wasu shaidun gani da ido.

Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia
Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia RFI-Swahili
Talla

Hare-haren sun faru ne a kudancin yankin Lower Shabelle a sansanonin da ke garuruwan Aw-dheegle da Bariire - kusan kilomita 30 tsakaninsu, Dukkaninsu biyu sansanoni da aka kafa don yakar kungiyar.

Babbabn Hafsan sojojin kasar Janar Odowa Yusuf Rage, da yake tabbatar da manema labarai hare-haren yace, "Maharan sun yi kokarin kai hari amma jajirtattun sojojisu wadanda suka san dabarun maharan, sun fatattaki 'yan bindigar kuma nan gaba kadan zasu yi Karin haske dangane da adadin mayaka da suka kashe da wadanda suka jikkata.

"Har yanzu sojojin na ci gaba da bin sawun sauran maharan kuma sojojin Somaliya na rike da iko da wuraren da aka fafata."

 

Shaidu a Awdheegle - mafi girma daga sansanonin biyu - sun ce sojojin Somaliya sun fatattaki 'yan bindigar bayan sun kwashe kusan awa guda suna gwabza kazamin fada.

"'Yan bindigar Shabaab sun yi amfani da wata mota dauke da abubuwa masu fashewa wajen kaddamar da harin, amma sun kasa shiga sansanin bayan sun kwashe kusan sa'a guda suna musayar wuta da sojojin Somaliya," in ji wani mazaunin garin Mohamed Ali ta wayar tarho.

"Na ga gawarwaki da yawa na 'yan bindigar Shabab a kusa da sansanin da fadan ya barke, sojojin Somaliya sun kwashe gawarwakin bayan fadan."

Al-Shabaab da dauki alhakin harin

Tuni Al-Shabaab, wacce ta dade tana tayar da kayar baya domin kawar da gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen duniya a Mogadishu, ta yi ikirarin daukar nauyin kai harin a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin intanet da ke goyon bayan kungiyar.

To sai dai Kungiyar ta yi ikirarin cewa ta kashe mutane da dama tare da kame motocin soja da kayayyaki.

An fatattaki Al-Shabaab daga Mogadishu a shekarar 2011, amma har yanzu suna iko da wasu yankuna daga inda suke shiryawa da kai hare-hare masu saurin kisa kan dakarun gwamnati da fararen hula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.