Isa ga babban shafi
Masar

Wasu jiragen kasa 2 sun yi karo da juna tare da hallaka mutane 32 a Masar

Akalla mutane 32 suka rasa rayukansu yayinda wasu 66 suka jikkata a wani hadarin jiragen kasa na fasinja guda biyu da suka yi taho mu gama da juna a kudancin kasar Masar yau Juma'a.

Fiye da mutane 60 suka jikkata a hadarin jirgin mafi muni da Masar ta gani a shekarun baya-bayan nan.
Fiye da mutane 60 suka jikkata a hadarin jirgin mafi muni da Masar ta gani a shekarun baya-bayan nan. REUTERS - STRINGER
Talla

Hadarin wanda ke matsayin mafi muni da kasar ta gani a baya-bayan nan, ma'aikatar lafiyar kasar ta ce tuni aka aike da jerin motocin daukar marasa lafiya tare da jami'an agajin gaggawa don kai dauki yankin da lamarin ya faru.

Bayanai sun ce Jiragen sun ci karo ne a kudancin Masar, daya daga cikin jiragen yana hanyar shi ne ta zuwa Luxor da Alqahira yayinda dayan jirgin kuma ya ke hanyar shi ta tafiya Cairo da kuma kudancin birnin Aswan.

Tuni dai shugaba Abdel Fattah al Sisi ya sha alwashin hukunta duk wadanda ke da hanu a haddasa afkuwar hadarin.

Hukumar kula da jiragen kasa ta Masar ta ce, wasu fasinjojin da ba asan ko su wanene ba sun yi ta yunkurin tsayar da jirgin ta hanyar janyo waigi ko kuma igiyar tsayar da jirgin na gaggawa wanda ya haddasa matsala ga birkin jirgin da ya kai ga karkacewarsa daga layin dogo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.