Dan asalin Najeriya ya katse aikinsa da shugaban Liberia
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Liberia wanda kuma dan asalin Najeriya ne, Ndubuisi Nwabudike ya sauka daga mukaminsa sakamakon zargin cewar ya bi ta bayan-gida wajen samun takardar zama dan kasa.
Wallafawa ranar:
Bayan takaddamar da ta kaure kan zargin, kotun kolin kasar ta gabatar da hukunci kan cewar Nwabudike bai saba ka‘ida ba wajen karbar takardun zama ‘dan kasa, amma hakan bai hana shi gabatar da takardar murabus dinsa ba.
Jami’in ya rubuta wa shugaban kasa George Weah wasikar cewar ba ya bukatar ci gaba da zamansa kan kujerar don kauce wa haifar da matsalar da za ta hana shugaban gudanar da ayyukansa, saboda haka ya sauka daga mukamin.
Nwabudike ya kwashe lokaci yana gudanar da bincike kan ayyukan cin hanci da rashawa a kasar a matsayinsa na lauya, kafin shugaban kasa Weah ya nada shi ya shugabanci hukumar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu