Isa ga babban shafi
Afrika

Taron samar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya a Angola

Shugabanin kasashen yankin Afrika ta tsakiya na gudanar da taron su a Luanda dake babban birnin kasar Angola da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika tun bayan da sojojin tareda hadin gwuiwar dakarun kasashen waje suka murkushe yan tawayen da suka yi kokarin sa kai zuwa babbani birnin kasar Bangui.

Taron sulhunta rikicin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika na shekara ta 2019 a Bangui
Taron sulhunta rikicin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika na shekara ta 2019 a Bangui https://twitter.com/UN_CAR
Talla

Taron na Angola na zuwa ne a wani lokaci da hukumar kula da ‘yan cin rani ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce zuwa yanzu mutane fiye da dubu dari 2 rikici ya raba da muhallansu a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ciki har da wasu fiye da dubu 100 a cikin kasar yayinda makamancin adadin suka tsere makwabtan kasashen.

 

Alkaluman na Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa dai dai lokacin da wasu bayanai ke cewa yanzu haka anfara wani wani zaman tattaunawa a Angola don kawo karshen rikicin Afrika ta tsakiyan da ke ci gaba da tsananta.

Wani mamba a kungiyoyin da ke kai agaji kasar Rabo Aliko ya mana tsokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.