Afirka ta Tsakiya ta saka dokar ta baci a fadin kasar
Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta saka dokar ta baci na kwanaki 15 a dai-dai lokacin da ‘Yan tawayen kasar suka kutsa kai birnin Bangui da nufin kiffar da zababben shugaban kasa Faustın Archange-Touadera.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Albert Yaloke Mokpeme ya ce dokar ta shafi yankin kasar baki daya zata kwashe kwanaki 15 tana aiki.
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar ya bukaci kwamitin sulhu da ya kara yawan dakarun samar da zaman lafiya dake aiki a kasar saboda barazanar ‘yan Tawayen.
Ana zargin tsohon Shugaban kasar Francois Bozize da kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar da yi watsi da takarar sa da tallafawa kungiyoyin yan tawaye a wannan tafiya don kwace ikon Bangui daga hannun Shugaban kasar Touadera.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu