Isa ga babban shafi
Duniya

‘Yan jaridun da Covid 19 ta kashe a Duniya sun kai 600

Wata kungiya mai zaman kanta dake tattara alkaluman ‘yan jaridun da suka mutu a sassan duniya, ta ce sama da manema labaran 600 annobar Coronavirus ta halaka daga watan Maris na 2020, zuwa karshen shekarar.

Wasu daga cikin ma'aikatan  gidan rediyo
Wasu daga cikin ma'aikatan gidan rediyo Géraud Bosman/RFI
Talla

Kungiyar mai suna PEC a takaice tace daga cikin jumillar ‘yan jaridu 602 da annobar ta korona ta aika barzahu a sassan duniya, 303 sun mutu ne a yankin Latin ko Kudancin Amurka kadai, 145 a Asiya, 94 a Turai, 32 a Amurka, sai kuma nahiyar Afrika da cutar ta halakawa manema labarai 28.

A matakin kasashe kuwa, maeman labarai 93 annobar ta Korona ta halaka a Peru, 55 a Brazil, 53 a Indiya, 45 a Mexico, sai 42 a Ecuador.

Bangladesh ta rasa ‘yan jaridu 41, Italiya 37, yayinda manema labarai 31 suka mutu a Amurka bayan kamuwa da cutar Korona.

Sai dai rahoton kungiyar sa idon ta PEC yace ba zai yiwuwa a iya tantance manema labaran da suka mutu suna kan aiki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.