Isa ga babban shafi
Afrika

Yan Adawa sun sa kafa sun yi fatali da sakamakon zaben Tsakiyar Afrika

Yan adawa a kasar jamhuriyar Afrika ta tsakkiya sun sa kafa sun yi fatali da sakamakon zabukan shugaban kasa da na yan majalisar dokokin da aka gudanar a ranar lahadi 27 ga watan Disamba da ya gabata.

Faustin-Archange Toudéra, Shugaban kasar Afrika ta tsakiya
Faustin-Archange Toudéra, Shugaban kasar Afrika ta tsakiya Ludovic MARIN / AFP
Talla

Nicolas Tiangaye kakakin yan adawar kasar ya bayyana zaben a matsayin zaben dake tattare da rudani.

Dan siyasar ya bukaci a sake gudanar da zaben, baiwa daukacin yan siyasar kasar damar shiga fagen siyasa hakan zai kuma taimaka domin dawo da zaman lafiya a kasar ta tsakiyar Afrika.

Nicolas Tiangaye ya ce ba a kirga kuri’un nan take a lokacin da aka kamala zaben ba, an yi shi ne a ranar ta biyu.

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD Minusca ce ta tattara akwatunan zaben a bayan idon wakilan yan takarar, abinda ya sabawa kundin zaben kasar.

Wakilan yan takarar zaben shugabancin kasa basu samu takardar dake kunshe da sakamako zaben da aka sakawa hannu ba, kamar yadda kundin zabe ya tanada.

Dazu nan ne sanarwa daga jam'iyyar shugaban kasar kuma dan takara Faustin Archange Touadera ta bayyana cewa Shugaban kasar ya kama hanyar lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.