Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

An gudanar da sahihin zaben shugaban kasa - Touadera

Gwamnatin Afrika ta Tsakiya ta ce, an gudanar da sahihin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a kasar duk da rahotanni da ke tabbatar da tashe-tashen hankula da suka mamaye zaben na ranar Lahadi.

Jami'an tsaro na gudanar da aikin tsaro a wata unguwar birnin Bangui
Jami'an tsaro na gudanar da aikin tsaro a wata unguwar birnin Bangui RFI/Charlotte Cosset
Talla

Yan lokuta da kammala zaben hukumar Zaben Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta bayyana yadda aka gaza gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a kashi 14 cikin 100 na mazabun kasar ranar Lahadin da ta gabata, sakamakon yadda kungiyoyin ‘yan tawaye masu dauke da makamai suka farwa masu kada kuri’a wanda ya tilasta kulle rumfunan.Kungiyoyin ‘yan tawaye masu dauke da makamai da ke rike da iko da kashi biyu bisa uku na kasar, sun hana tarin jama’a fitowa domin kada kuri’unsu cikin ruwan sanyi.

Amma kakakin gwamnatin kasar, ya shaida wa manema labarai cewa, an yi sahihin zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.