Isa ga babban shafi

Kasashen duniya sun taimaka wa Najeriya wajen kubutar da daliban Kankara - Minista

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce kasar ta samu taimakon kasashen waje wajen kubutar da daliban makarantar Sakandaren Kankara 344 da aka sace daga makarantar su.

Lai Mohammed Ministan labaran Najeriya.
Lai Mohammed Ministan labaran Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja, ministan ya ce Najeriya na gode wa duk wadanda suka taka rawa wajen ganin an kubutar da yaran da ran su, a ciki da wajen Najeriya.

Ministan wanda yaki bayyana kasashen da suka taimaka wa Najeriya, ya ce koda sisin kwabo ba’a biya ba a matsayin diyya wajen sakin daliban, yayin da ya yaba rawar da jami’an tsaron Najeriya suka taka cikin lamarin.

Mohammed yayi watsi da zargin cewar boko haram ne ta kwashi yaran kamar yadda shugabanta Abubakar Shekau ya sanar a bidiyo, inda ya sake jaddada cewar 'yan bindiga ne suka kwashe su.

Ministan ya kuma karę matsayin gwamnati na tattaunawa da 'yan ta’adda idan hakan ya zama wajibi, inda ya ke cewa babu wata gwamnati a duniya da ba ta yin haka idan bukatar haka ta taso.

Dangane da zargin cewar shugaban kasa bai nuna damuwa kan lamarin ba, ministan yayi watsi da zargin, inda ya jaddada cewar shugaba Buhari ne ya jagoranci duk matakan da aka dauka wajen kubutar da daliban cikin kankanin lokaci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.