Isa ga babban shafi
Mauritania

Tsohon shugaban kasar Mauritania Sidi Ould Abdullahi ya rasu

Tsohon Shugaban kasar Mauritania Sidi Ould Cheikh Abdullahi ya rasu daren jiya yana da shekaru 82 a duniya sakamakon rashin lafiyar dake da nasaba da zuciya.

Wasu magoya baya rike da hoton tsohon hambararren shugaban Mauritania Sidi Ould Cheikh Abdallahi wanda ya rasu daren jiya Lahadi.
Wasu magoya baya rike da hoton tsohon hambararren shugaban Mauritania Sidi Ould Cheikh Abdallahi wanda ya rasu daren jiya Lahadi. Reuters
Talla

Iyalan tsohon shugaban da kuma fadar shugaban kasa sun sanar da cewar Abdallahi wanda shine zababben shugaban kasa na farko a kasar ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kan sa dake birnin Nouckchott.

An dai zabi tsohon shugaban ne ya kuma kama aiki a watan Afrilun shekarar 2007, kafin Janar Mohammed Ould Abdel Aziz ya kifar da gwamnatin sa bayan watanni 15 kacal a karagar mulki.

Janar Abdel Aziz ya zargi marigayin da gazawa wajen daukar mataki mai tsauri kan Yan bindigar dake danganta kan su da addinin Islama, yayin da ya kwashe shekaru 10 a karagar mulki.

Bayan juyin mulkin, marigayin yaki amincewa da halarcin gwamnatin sojin, abinda ya sa aka daure shi na dogon lokaci, kafin daga bisani aka masa sakin talala a gidan sa dake kauyen Lemden a shekarar 2008 har zuwa watan Yuni shekarar 2009 da ya janye daga harkokin siyasa.

Gwamnatin Mauritania ta bayyana zaman makoki na kwanaki 3 sakamakon rasuwar tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.