Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Ana bukatan dala miliyan 200 don taimakawa 'yan gudun hijirar Habasha - MDD

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka ce ana bukatar kimanin dala miliyan 200 don ba da tallafin gaggawa ga dubban ‘yan gudun hijirar da ke fitowa daga Habasha domin neman mafaka a Sudan.

Wasu 'Yan gudun hijirar Habasha dake neman mafaka a makwabta
Wasu 'Yan gudun hijirar Habasha dake neman mafaka a makwabta AP Photo/Marwan Ali
Talla

Yanzu haka sama da mutane dubu 300 suka tsallaka iyakar, yayin da Majalisar Dinkin Duniyar ke cewa adadin masu tserewa rikicin na Habasha zai iya kaiwa dubu 200 nan da watanni 6 masu zuwa.

Franministan Habasha Abiy Ahmed da ya karbi kyautan zaman lafiya ta Nobel a bara, ya kaddamar da farmakin soji yankin na Tigray da nufin kawar da jam’iyyar TPLF dake mulkin yankin da yake zargi da ya yiwa gwamnatin kasar zagon kasa.

A ranar Jumma'a mayakan tawayen yankin Tigray na kasar Habasha sun harba rokoki makwabciyarsu Eriteria, lamarin da ke haifar da fargabar yakin ya yadu zuwa kasashe makwabta, yayin da rundunar sojin Habasha ta sanar da cewa tana daf da mamaye birnin Mekele.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.