Isa ga babban shafi
Afrika

Yaki ya ta’azzara a arewacin Habasha

Yaki na ci gaba da ta’azzara a arewacin Habasha a yayin da a duk rana Sudan na karbar ‘yan gudun hijira dubu 3 da ke tsalaka kogin Tekeze, wanda ke iyaka da Sudan da Eritrea don su tsira da rayuwarsu.

Wasu daga cikin 'yan Habasha mazauna yankin Tigray da suka tserewa muhallansu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsaknin sojoji da 'yan tawayen jam'iyyar TPLF
Wasu daga cikin 'yan Habasha mazauna yankin Tigray da suka tserewa muhallansu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsaknin sojoji da 'yan tawayen jam'iyyar TPLF AFP
Talla

Yawan ‘yan gudun hijiran daga Habasha dai sai karuwa yake yi, inda aka jibge su a wani sansani da aka taba jibge su a sherun 1980 a lokacin da ‘yan Habashan suka yi fama da matsanancin fari.

Aisir Khaled shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Kassala dake Sudan, yana ganin yadda ‘yan Habasha ke tururuwan zuwa sansanin , ya zuwa yau Juma’a aka sami ‘yan gudun hijira dubu 20.

Yawancin ‘yan gudun hijiran dai yara ne kanana, da mata da matasa dake neman kauracewa kazamin tarzoman da ake fafatawa na tsawon mako daya a kasar ta su.

Wasu ‘yan gudun hijiran a wahalce, kan rika hutawa a hanyarsu ta shiga kasar Sudan, bayan da suka yi tattaki zuwa wani kogi, dake tsakanin kasashen biyu.

01:43

Yaki ya ta’azzara a arewacin Habasha

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.