Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaba Magafuli ya lashe zaben Tanzania

Hukumar zaben Tanzania ta ayyana Shugaban Takasar kuma dan takara John Magufuli mai shekaru 61 a matsayin wanda ya lashe zaben kasarda kusan kashi 84 da dingo 39 na kuri’u da aka kada ,gaban abokin hamayar sa Tuhdu Lissu bangaren adawa mai shekaru 52 .

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli.
Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli. AP Photo
Talla

A baya,babban Jam’iyyar adawar Tanzania ta ce ba za ta amince da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi jiya ba, saboda zargin tafka magudin da ta ce anyi wanda ya bai wa Jam’iyya mai mulki damar lashe kujerun majalisu mafi muhimmanci a kasar.

Rikici ya soma kuno kai ne bayan da Hukumar zaben Tanzania ta ce sakamakon farko daga mazabu 12 daga cikin 264 sun nuna cewar shugaba John Magufuli da ke neman wa’adi na biyu na kan gaba da kashi 80 wajen ganin Jam’iyyar sa ta Chama Cha Mapinduzi ta ci gaba da rike mulki tun daga shekarar 1961.

Sakamakon ya nuna cewar babban dan adawa Tundu Lissu na bi masa da kashi 15, kuma tuni ya bayyana sakamakon a matsayin haramtacce ya kuma bukaci magoya bayan sa da su gudanar da zanga zangar lumana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.