Isa ga babban shafi
Guinea

Amnesty ta zargi jami'an tsaron Guinea da kisan tarin masu zanga-zanga

Kungiyar Amnesty International ta zargi jami’an tsaron kasar Guinea da harbin masu zanga zanga da harsasai masu rai abinda ya yi sanadiyar hallakar mutane da dama a cikin kasar.

Masu zanga-zangar adawa da nasarar shugaba Alpha Conde a zaben kasar da zai bashi damar shugabanci a karo na 3.
Masu zanga-zangar adawa da nasarar shugaba Alpha Conde a zaben kasar da zai bashi damar shugabanci a karo na 3. REUTERS/Saliou Samb NO RESALES
Talla

Sanarwar da kungiyar ta gabatar ta ce shaidun da suka tattara bayanai da kuma hotunan bidiyo sun tabbatar da zargin, wandanda kungiyar ta ce sun nuno karara yadda jami'an kasar ta Guinea suka hallaka tarin fararen hular.

Amnesty International ta kuma zargi gwamnati da katse hanyar sadarwar intanet a lokacin zanga zangar don kalubalantar shugaba Alpha Conde.

Tuni dai hukumar zaben Guinea ta bayyana shugaba Alpha Conde mai shekaru 82 a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da akayi da kuri’u kusan kashi 60, yayin da shugaban 'yan adawa Cellou Dalein Diallo ya ce zai kalubalanci sakamakon.

Conde wanda ya samu zarafin takara a zaben da ya bashi damar zarcewa a karagar mulki bayan kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar da ya bashi damar yin wa'adi na 3, tun bayan sanar da matakin al'ummar kasar ke bore don kalubalantarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.