Isa ga babban shafi

'Yan awaren Ghana sun kai hari tare da kona motaci a tasha

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'Yan aware ne dake neman kafa kasa ta kan su a Ghana sun kai hari kan wata tashar mota, inda suka kona mota guda a garin Ho dake yankin Volta.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo. REUTERS/Francis Kokoroko
Talla

Rahotanni sun ce maharan sun bude wuta lokacin harin, kafin suyi garkuwa da wani mai gadi, bayan sun lakadawa wasu direbobi duka.

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan wanda aka kai jami’an tsaro, abinda ya kaiga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

A farkon makon nan Rundunar  Soji da Yan Sanda a Ghana sun sanar da kashe wani dan kungiyar Yan aware dake neman ballewa domin kafa kasa ta kan su, bayan sun kaiwa ofishin Yan Sanda hari.

Sanarwar hadin gwuiwar da dakarun biyu suka sanya hannu akai tace sakamakon harin da ‘yayan kungiyar Yan awaren ta HSGF suka kaiwa ofishin Yan Sandan, sun yi musayar wuta da su, inda suka kasha mutuum guda da kuma kama wasu 31.

Su dai ‘yan awaren sun kaddamar da yunkurin kafa kasar Western Togoland ne tun daga shekarar 1970.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.