A karon farko mace ta zama yar takarar mataimakiyar shugabancin kasa a Ghana
A karon farko babbar jam’iyyar NDC mai adawa ta Kasar Ghana ta zabi Jane Naana Opuku-Agyemang a matsayin mataimakiyar tsohon Shugaban Kasar, John Dramani Mahama a zaben shugabancin Kasar da ake shirin gudanarwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ranar 7 ga watan Disemba na shekarar 2020 ne za a gudanar da zaben kasar Ghana,yayinda suka rage yan watanni,daukacin jam'iyyoyin siyasa na ta kokarin samun goyan baya da ya dace don samun nasarar zaben.
Daga bangaren adawa,a karkashin tsohon Shugaban kasar John Dramani Mahama,mutumen da yan adawa suka tsayar da shi a matsayin dan takarar su a jam'iyyar NDC,wannan dai ne karo na uku da Shugaban kasar mai ci da na bangaren adawa John Mahama suke fafatawa a zaben kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu