Isa ga babban shafi
Afrika-Turai

An garzaya da Felicien Kabuga asibiti a Paris

Daya daga cikin mutanen da suka tallafa a yakin kasar Rwanda da kuma ke tsare a Faransa yanzu haka, Felicien Kabuga na samu kulawa daga likitoci ,bayan da aka gano cewa ya na fama da rashin lafiya.

Félicien Kabuga dake fuskantar tuhuma a Faransa
Félicien Kabuga dake fuskantar tuhuma a Faransa Nations Unies/AFP
Talla

Ranar 30 ga wannan watan ake sa ran alkalai a Faransa za su gudanar da zaman su don tattance yiyuwar mika shi zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya.

Wata majiya a Faransa na bayyana cewa an garzaya da shi zuwa wani asibiti dake Paris inda ake sa ran likitoci za su kula da shi.

Indan aka yi tuni ranar 3 ga watan yuni na shekarar bana ne kasar sa ta asali Rwanda ta shigar da bukata ga hukumomin Faransa don mika shi zuwa kotun hukunta manyan laifuka,bayan da aka kam shi ranar 16 ga watan mayu.

Felicien Kabuga mai shekaru 87 na fuskantar tuhuma ta hada baki wajen kaffa rundunar yan sa kai a karkashin kabilar Hutu, tareda tunzura jama’a zuwa ga daukar makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.