Isa ga babban shafi
Libya

Masu zanga-zanga sun cinnawa hedikwatar gwamnati wuta a Benghazi

Masu zanga-zanga a Libya sun bankawa hedikwatar gwamnatin birnin Benghazi wuta, bayanda da zanga-zangar dake gudana kan neman inganta yanayin rayuwa da kuma yakar rashawa ta rikide zuwa tarzoma.

Daya daga cikin hanyoyin da masu zanga-zanga suka datse a garin Benghazi
Daya daga cikin hanyoyin da masu zanga-zanga suka datse a garin Benghazi AFP
Talla

A daren jiya Asabar zanga-zangar ta soma a garin Al-Bayda inda a baya gwamnatin Libya ke da Hedikwata, daga bisani kuma boren ya bazu zuwa biranen Sabha, da kuma Al-Marj, inda Janar Khalifa Haftar mai iko da gabashin kasar yafi karfi.

A karshen watan Agusta makamanciyar zanga-zangar ta barke a yammacin kasar ta Libya dake karkashin ikon gwamnatin hadin gwiwar da majalisar dinkin duniya ke marawa baya.

A shekarar 2014 Libya ta rabu zuwa gida 2, bangaren gabashi dake karkashin ikon Janar Khalifa Haftar da kuma Yammaci dake karkashin ikon gwamnatin da majalisar dinkin duniyar ke marawa baya, wadda Haftar ke kokarin kifarwa bayan farmakin da ya kaddamar kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.