COVID 19: Za a sake bude wuraren ibada a Lagos
Gwamnan Legas a Najeriya, Babajide Sanwo-Olu ya bada umarnin sake bude wuraren ibada a daukacin jihar, bayan da suka shafe watanni a rufe, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Wallafawa ranar:
Yayin sanar da matakin a yau asabar, Sanwo-Olu ya ce matakin sake bude wuraren Ibadar zai soma aiki ne daga 7 ga watan Agustan da muka shiga, amma da sharadin kashi 50 cikin 100 na adadin mutanen da filaye ko gine-ginen da wuraren ibadar za su iya dauka ke da izinin shiga cikinsu.
Gwamnan na Legas ya kuma sassauta dokar da ta haramta taron sama da mutane 20 zuwa sama da mutane 50.
Sanwo-Olu ya kuma shawarci dattawa masu shekaru 65 zuwa sama da su kaurce wa wuraren ibada.
A watan Maris ne hukumomin Legas, birni mafi girma a Najeriya mai mazauna miliyan ashirin suka rufe coci coci da masallatai, wuraren shakatawa da sauransu, a kokarin d suke na dakile yaduwar cutar coronavirus.
Ya zuwa yanzu cutar ta harbi mutane dubu 43 da dari da 51, ta kuma kashe dari 8 da 79 tun da ta shiga Najeriya a watan Fabrairu.
Jihar Legas ce cutar ta fi kamari a Najeriya, inda mutane dubu 15 suka harbu, dari da 92 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu