Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Lagos tana kashe naira miliyan 1 kullum kan masu corona

Gwamnatin jihar Lagos a Najeriya ta yi karin bayani kan ikirarin da ta yi tun da farko cewa tana kashe kudin da ya kai Naira dubu dari 5 zuwa miliyan 1 duk rana wajen yi wa masu fama da cutar COVID 19 wadanda ke cikin mawuyacin hali magani.

kwayar cutr coronavirus kamar yadda na'ura ta dauko.
kwayar cutr coronavirus kamar yadda na'ura ta dauko. NEXU Science Communication/via REUTERS
Talla

Tun d farko jaridun kasar sun ruwaito kwamishinan lafiya na jihar, Akin Abayomi yana cewa a wata sanarwa, Naira dubu 100 ne jihar ke kashewa wajen yi wa wadanda cutar ba ta yi mummunan tasiri a jikinsu ba magani, wadanda cutar ta kama sosai kuwa ana kashe Naira dubu dari 500 zuwa miliyan 100 kowace rana.

‘Yan Najeriya da dama sun caccaki wannan sanarwa ta kwamishina, inda suke zargin jihar da barnata kudin al’umma, har ma wasu na kira da a yi musu cikakken bayani kan yadda ake kashe irin wadannan kudade.

Hakan ne ma ya sa a Juma’ar, nan kwamishinan yada labaran jihar Gbenga Omotosho ya fitar da wata sanarwa da zummar karin bayani, yana mai cewa an yi wa kwamishinan lafiya mummunar fahimta.

Mr Omotosho, wanda yake a taron manema labaran da kwamishinan lafiyar ya yi bayanin kudaden da ake kashewa kan masu corona ya ce, ministan lafiyar yana kokari ne ya nuna yadda ake samun yanayi na tsanani da kuma sauki a tattare da masu fama da cutar.

Omotosho ya jaddada cewa lallai gwamnatin jihar na kashe wadannan kudade a wajen yi wa masu fama da wannan cuta magani, sai dai wadanda suka yi tsanani ba su da yawa, mutane dari 2 ne kawai cikin sama da dubu 2 da ke kwance a asibiti ake kashe Naira miliyan daya duk rana wajen yi musu magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.