Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

Najeriya:'Yan bindiga sun yi awon gaba da shanu 500 a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki kan garin Wara-Wara dake karamar hukumar Tsafe, inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi.

Mutane 9 ne suka jikkata a wannan samame da 'yan bindiga suka kai wani kauye a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Mutane 9 ne suka jikkata a wannan samame da 'yan bindiga suka kai wani kauye a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara. shakarasquare
Talla

Majiyar da muka zanta da ita, ta shaida mana cewar, maharan sun afkawa garin na Wara - Wara ne da maraicen jiya asabar haye kan babura akalla 15, inda suka kore dabbobi akalla 500.

Majiyar ta ce ba a samu hasarar rai yayin harin ba, sai dai akalla mutane 9 sun jikkata, yayin da suke kokarin gudun tsira.

Jihar Zamfara dake arewa maso yammncin Najeriya na daga cikin jihohin da ke fama da hare haren ‘yan bindiga, barayin shanu da masu satar mutane don karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.