Isa ga babban shafi
Najeriya

Sarkin Gusau ya zargi wasu al'ummar Zamfara da taimakawa 'Yan bindiga

Sarkin Gusau da ke Jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Bello ya yi zargin cewar wasu ‘yan Jihar na taimakawa 'yan bindiga barayin shanu da masu garkuwa da mutane wajen samar musu da gidajen haya ko kuma sayar musu da gidajen zaman.

Wasu 'yan bindiga da suka addabi Arewa maso yammacin Najeriya.
Wasu 'yan bindiga da suka addabi Arewa maso yammacin Najeriya. Daily Trsut
Talla

Yayin da ya ke gabatar da jawabi a taron tsaron da aka gudanar a jihar wanda ya samu halartar Sufeto Janar na 'yan sanda Muhammadu Adamu da darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya Yusuf Bichi, Basaraken ya ce a matsayin su na Sarakuna sun gudanar da tarurruka da dama akai inda suka fahimci cewar ana samun bata gari da ke hada kai da irin wadannan mutane da suka addabi jihar.

Sarkin ya ce mutanen kan kwana a cikin su amma da safe sai su sulale inda suke zuwa aikata laifuffuka.

Basaraken ya ce idan anyi amfani da bayanan asiri wajen gano wadannan batagarin da ke sayar musu da gidaje, zai taimaka wajen kama barayin da masu garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.