Isa ga babban shafi
Kenya

Wani jami'in tsaro ya aikata fyade a cibiyar killace masu corona a Kenya

‘Yan sanda a Kenya sun sanarda kame wani ma’aikacin gidan yari da ake zargin da yi wa wata mata fyade a cibiyar killace masu fama da cutar coronavirus da yake gadi.

Uhuru Kenyatta, Shugaban kasar Kenya.
Uhuru Kenyatta, Shugaban kasar Kenya. REUTERS/Njeri Mwangi/File Photo
Talla

Wannan ne matsalar baya baayan nan da aaka samu a daya daga cikin cibiyoyin killace masu cutar corona da gwamnatin kasar ta samar, wadanda ake korafin basu dace akawi matsaloli na rashin kulawa a cikinsu.

Kwararru a fannin lafiya sun ce aukuwar irin wannan al’amari zai hana al’umma gabataar dakaanssu ko da sun ji alamun cutar a tattare da su.

A farkon wannan shekarar an yi ta samun matsalolin marasa lafiya da ke tserewa daga cibiyoyin killace masu fama da cutar Covid 19 biyo bayan koke koken rashin isasshen abinci, ruwan sha da rashin tsabtataccen muhalli.

A watan Maris, hukumomi sun ce suna bincike kan mutuwar wani d aka ce ya kashe kansa ne a daya daga cikin cibiyoyin killacewa.

Wannan al’amari na fyade ya auku a dayaa daga cikin cibiyoyin killace masu wannan cuta da ke garin Busia a iyakar kasar, inda ‘yan sanda d jami’an gidan yari ke d alhakin tsaron lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.