Isa ga babban shafi
Kenya

'Yan sandan Kenya 3 sun shiga komar hukuma kan dukan wata Mace

Hukumomin kasar Kenya sun kama wasu 'yan Sanda guda 3 da aka nada a faifan bidiyo suna jan wata mata a kasa da suka daure hannayen ta a jikin babur suna kuma zabga mata bulala saboda zargin da ake mata na aikata sata.

Wasu jami'an tsaro a Kenya.
Wasu jami'an tsaro a Kenya. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Kama jami’an ya biyo bayan korafin jama’a kan yadda Yan Sanda ke cin zarafin Bila dama sakamakon kisan gillar da Yan Sanda suka yiwa George Floyd a kasar Amurka.

Faifan bidiyon na minti guda da rabi ya nuna matar kwance a kasa ana janta a jikin babur, yayin da wasu Yan Sanda kuma na mata bulala har sanda wandan ta ya sabule.

Rahotanni sun ce ana zargin matar ne da shiga gidan wani dan sanda domin yin sata.

Daraktan kula da bincike na rundunar Yan Sandan yace an kama jami’an guda 3 a Kuresoi kuma ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ko a ranar litinin da ta gabata akalla mutane 200 suka gudanar da zanga zanga a birnin Nairobi kan yadda Yan sandan suka kashe mutane 15 lokacin da aka kafa dokar hana fita gida saboda yaki da annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.