Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta koma ta 3 a yawan masu dauke da coronavirus a Afrika

Bayan samun karuwar mutum 573 sabbin kamuwa da coronavirus a jiya da ya mayar da jumullar masu dauke da cutar dubu 16 da 658 a Najeriya, yanzu kasar ke matsayin ta 3 a yawan masu dauke da coronavirus a nahiyar Afrika bayan Afrika ta kudu mai yawan mutum dubu 73 da 533 a matsayin ta 1 da kuma Masar mai yawan mutum dubu 46 da 289 masu cutar ta COVID-19.

Wasu jami'an lafiya da ke aikin gwaji a dakin gwajin cutuka na Asibiti.
Wasu jami'an lafiya da ke aikin gwaji a dakin gwajin cutuka na Asibiti. Photo: Seyllou/AFP
Talla

Hukumar kula da yaduwar cutuka ta Najeriyar NCDC ta ce sabbin kamuwar 216 na jihar Lagos kana 103 a Rivers sai wasu 68 a Oyo tukuna 40 a Edo kana 21 a Kano sai wasu 20 a Gombe 17 kuma a Abuja tukuna 13 a Delta, sai 12 a jihohin Plateau da Bauchi kana 10 a Niger.

Sauran sun hada da 9 a Kebbi, 8-8 a Ogun da Ondo, 7 a Abia, 5 a Nasarawa, kana guda guda a Jihohin Borno, Kwara, Benue da Anambra.

Cutar ta coronavirus wadda ta fantsama a ilahirin kasashen nahiyar Afrika, yanzu haka akwai jumullar mutum dubu 242 da 969 masu dauke da ita, ciki kuwa har da mutum dubu 6 da 524 da ta kashe inda ake da mutane dubu 110 da 735 da suka warke.

Har yanzu Afrika ta Kudu ce jagora a yawan amsu cutar da mutane dubu 73 da 533 kana Masar da mutane dubu 46 da 289 tukuna Najeriyar da yawan masu dauke da cutar dubu 16 da 658.

Sauran kasashen na Afrika masu yawan mutanen da ke dauke da cutar ta coronavirus sun hada da Ghana mai yawan mutane dubu 11 da 964 tukuna Algeria da masu dauke da cutar dubu 11 da 31.

Hukumar lafiya ta duniya WHO dai na ganin matukar kasashen na Afrika basu tashi tsaye tare da daukar matakan da suka dace a yaki da cutar ba, babu shakka za a iya samun miliyoyin masu dauke da COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.