Isa ga babban shafi

Tsohon Franminista ya biya kudi don kasashe matarsa - Yan sanda

'Yan Sanda a Malawi sun ce tsohon Firaministan kasar Thomas Thabane ya biya mutanen da ya dauki hayar su domin kashe tsohuwar matar sa dala 24,000 domin raba ta da ran ta.

Tsohon Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane da maidakinsa
Tsohon Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane da maidakinsa Photo: Samson Motikoe/AFP
Talla

Bayanan na baya bayan nan sun dada fito da rawar da tsohon Firaministan ya taka abinda ya sa aka tilasta masa sauka daga mukamin sa domin fuskantar shari’a.

Thabane tare da tsohuwar matar sa sun fada cikin mummunar rikici lokacin da ya nemi a raba auran dake tsakanin su, yayin da yan bindiga suka harbe ta har lahira kwana biyu kafin rantsar da shi a shekarar 2017.

Ya zuwa yanzu dai ba’a gurfanar da tsohon Firaministan a kotu ba, amma kuma binciken Yan Sanda ya nuna cewar yana da hannu wajen kisan kuma tuni aka kama amaryar sa Maesaiah wadda ke tsare a ofishin Yan Sanda.

Kwamishinan Yan Sanda Paseka Mokete yace Thabane ya bukaci kashe tsohuwar matar ne domin baiwa amaryar damar zama ‘First Lady’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.