Isa ga babban shafi
Kamaru-Boko Haram

An gano gawar mutane 3 cikin 21 da Boko Haram ta sace a Kamaru

A kasar Kamaru an gano gawarwakin mutane uku da ‘yan Boko Haram suka sace tun ranar Alhamis din da ta gabata a wani gari mai suna Tokomari da ke cikin gundumawar Kolafata kusa da iyakar kasar da Najeriya.

Wasu dakarun sojin kasar Kamaru.
Wasu dakarun sojin kasar Kamaru. Edwin Kindzeka Moki/AP/SIPA
Talla

Bayanai sun ce daga cikin mutanen uku da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kashe har da mace daya, kuma dukanninsu an yi masu yanka rago ne.

Majiyoyin tsaron Kamaru da suka tabbatar da farmakin na ranar Alhamis sun bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun yi garkuwa da fararen hula akalla 21 gab da kan iyakar kasar da Najeriya mai fama da rikicin ta’addanci.

Majiyar tsaron ta tabbatar da cewa 4 cikin mutanen da aka yi garkuwa da su sun yi nasarar kubuta yayinda kawo yanzu ba a san halin da sauran mutanen ke ciki ba.

Cikin sauran mutanen da suka rage a hannun mayakan na Boko Haram a yanzu haka harda mata da kuma kananan yara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.