Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya hana bahaya a bainar jama'a

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta yin bayan gida a bainar jama’a.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Sanarwar da mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya raba wa manema labarai ta ce dokar mai lamba 009 za ta hukunta duk wanda aka samu da laifin yin bayan gida a bainar jama’a saboda illar da ta ke yi wa harkar kula da lafiyar al’umma.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Najeriya ce kasa ta biyu bayan Indiya da jama’ar ta ke yin bayan gida a bainar jama’a.

Alkalumma sun ce mutane miliyan 46 daga cikin ‘yan Najeriya kusan miliyan 200 ba su da wajen bayan gida da za su kebe idan bahaya ta kama su.

Dokar ta baiwa ma’aikatar samar da ruwan sha umurnin tabbatar da cewa daga yanzu ya zama dole duk makarantu da otel otel da gidajen mai, da wuraren ibada da kasuwanni da asibitoci su samarwa jama’a wurin yin bayan gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.