Isa ga babban shafi
DR Congo-Ebola

Ministan lafiyar Congo na fuskantar tuhuma kan sace kudin yakar Ebola

Tsohon Ministan lafiyar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Oly Ilunga ya shiga hannun hukuma biyo bayan zargin da ya ke fuskanta kan karkatar da kudaden asusun yaki da cutar da Ebola da kasar ke fuskantar annobarta.

Akwai dai bayanan da ke nuna cewa wawure kudin yaki da cutar ya taka muhimmiyar vawa wajen haddasa koma baya a yakin da ake da ita.
Akwai dai bayanan da ke nuna cewa wawure kudin yaki da cutar ya taka muhimmiyar vawa wajen haddasa koma baya a yakin da ake da ita. Reuters/Baz Ratner
Talla

Sanarwar rundunar ‘yan sandan kasar ta nuna cewa Ilunga wanda ya yi murabus cikin watan Yulin da ya gabata, bayan cire daga mukamin shugaban yaki da cutar Ebola a kasar, an yi nasarar kama shi ne a wani rukunin gine-gine da ke Kinshasa babbar birnin kasar a kokarinsa na ficewa daga Congon don kaucewa tuhuma.

A zantawar Kanala Pierrot-Rombaut na rundunar ‘yansandan da kamfanin dillancin labaran Faransa, ya bayyana cewa Dr Ilunga ya karkatar da makudan kudade wadanda suka haddasa koma baya a yakin da kasar ke yi da annobar cutar Ebola.

Tuni dai aka haramtawa Ilunga mai shekaru 59 fita daga kasar yayinda zai gurfana gaban kotu a ranar Litinin ko da dai tun a watan Agusta ya musanta zargin karkatar da kudaden yakar Ebola wadda kawo yanzu ta hallaka mutane dubu 2 a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.