Isa ga babban shafi
Tanzania

Mutane 64 sun mutu a gobarar tankar man fetir

Akalla mutane 64 sun rasa rayukansu, yayinda 70 suka jikkata bayan wata tankar dakon man fetir ta wuntsula sannan ta kama da wuta a Tanzania, kamar yadda jami’an ‘yan sandan kasar suka sanar.

Wurin da tankar man fetir ta kama da wuta a garin Morogoro na Tanzania.
Wurin da tankar man fetir ta kama da wuta a garin Morogoro na Tanzania. REUTERS TV
Talla

Bayanai na cewa, jama’a sun doshi tankar ce domin kwasar ganimar man fetur jim kadan da faduwarta a garin Morogoro mai tazarar kilomita 200 daga yammacin birnin Dares Salam a yau Asabar.

Gwamnan Morogoro ya ce, tuni aka jibge gawarwakin mutanen 64 a asibiti, yayinda ya gargadi cewa, adadin mamatan ka iya karuwa nan gaba.

Hotunan da aka yada sun nuna yadda hayaki ya turnuke sararin samaniya sakamakon gobarar yayinda a gefe guda, hotunan suka nuna mutane dauke da jarkokin man fetir a kusa da tankar.

Shugaban kasar, John Magufuli da sauran fitattun jama'ar kasar sun aike da sakon ta'aziyarsu, yayinda shugaba Magufuli ya bukaci mutane da su rika kauce wa kwasar ganimar man fetir a irin wannan yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.