Isa ga babban shafi
Sudan

Gwamnatin Sojin Sudan ta gargadi masu shirin zanga-zanga

Gwamnatin mulkin soji a Sudan ta gargadi fararen hula game da wani shirin sake tsunduma zanga-zangar adawa da matakan gwamnatin a yau Lahadi, inda ta fitar da sanarwar cewa jagororin masu zanga-zangar da bangaren adawa za su dandana kudarsu matukar su ka kai ga asarar rai ko dukiya a zanga-zangar ta yau.

Wasu masu zanga-zanga a Sudan
Wasu masu zanga-zanga a Sudan REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Jagororin masu zanga-zangar a Sudan dai sun kira ga miliyoyin al’ummar kasar kan su fito manyan titunan birnin Khartoum don matsa lamba ga gwamnatin sojin wajen ganin lallai ta amince da mika mulki ga fararen hula.

Sai dai cikin sanarwar gwamnatin Sojin ta ce babau shakka za ta dauki tsauraran matakai kan mashirya zanga-angar matukar aka fuskanci asarar rai ko duniya yayin gudanar da gangamin.

Matakin zanga-zangar na zuwa dai dai lokacin da majalisar sojin Sudan ta amince da shirin kafa gwamnatin wucin gadi a kasar da hadin gwiwar kungiyar kasashen Afirka AU da kuma Habasha ya gabatar.

Shirin sulhun ya kunshi kafa majalisar zartaswar gwamnatin hadaka mai kunshe da wakilan fararen hula 8, na sojoji 7, sai dai babu Karin haske kan adadin wakilan bangarorin da sabuwar majalisar kasar za ta kunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.