Isa ga babban shafi
Afrika

An rantsar da Buhari da Osinbajo a Najeriya

A yau Laraba 29 ga watan Mayu aka rantsar da Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC a matsayin  shugaban Najeriya a wani sabon wa'adi na biyu.Shugaba Buhari ya karbi rantsuwar ne a Abuja dake birnin tarraya,inda ya dau alkawali na gudanar da mulkin bisa gaskiya da adalci.

Rantsar da Buhari a Abuja
Rantsar da Buhari a Abuja rfi hausa
Talla

Alkalin alkalai mai shari’a  Tanko Mohammed ne ya rantsar da Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da safiyar yau Laraba.

Wakilan kasashen duniya da dama ne suka halarci bikin rantsar da Buhari a Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

Rahotanni sun ce an girke Sojoji a hanyoyin shiga Abuja tare da girke ‘Yan sanda a sassan birnin da suka hada da gine ginen Gwamnati.

Buhari ya taba rike mukamin Shugaban kasa a mulkin Soja shekaru 36 da suka gabata,kafin daga bisani ya lashe zaben shekara ta 2015 a zaben da ya doke Goodluck Jonathan.

A zaben shekara ta 2019,Shugaba Buhari ya doke dan takara na jam'iyyar adawa Atiku Abubakar,wanda ya kuma shigar da kara a kotu tareda bukatar kotu ta soke zaben.

Bayan lashe zaben da ya hada shi da dan takara Atiku Abubakar a watan Maris, Buhari ya ce zai tabbatar da shugabanci na gari tare da bin tsari na dimokuradiya wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Babban kalubale da ke gabansa shi ne cika alkawullan da Jam’iyyarsa ta APC ta dauka na tabbatar da canji a kasar, wanda da dama daga cikin yan kasar suka bayyana rashin gamsuwar su dangane da yada ya tafiyar da wa'adin sa na farko.

Buhari wanda sananne a bangaren yaki da Rashawa ya nanata cewa wannan karo ,jama'a zasu ga canji, gwamnatinsa ba za ta yi cudanya da rashawa ba.

Buhari wanda tsohon Soja ne ya jaddada cewa zai jagoranci Yaki da Boko Haram tare da samar da wani tsari da zai karfafawa Sojoji guiwa da magance rashawa da ta dabaibaye rundunar sojin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.