Isa ga babban shafi
Afrika

Boko Haram ta kashe mutane 11 a Kamaru

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa mayakan Kungiyar Boko Haram sun kai wani kazamin hari cikin daren da ya gabata, in da suka kashe wasu mutane akalla 11 da ke barci.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram pmnewsnigeria
Talla

Wani dan kato da gora ya tabbatar da wannan hari da aka kai a yankin Tchakamari kuma tuni maharan suka tsere bayan aika-aikar.

Bayaga kisan jama'a, ‘mayakan  sun kuma kona kayen kurmus.

Mayakan sun shafe kimanin sa'o'i uku suna tabargaza kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.

Tun shekara ta 2009, Kungiyar Boko Haram ke cin karanta babu babbaka a yankin tafkin Chadi da ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

Rikicin na Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 30, yayinda mutane kusan miliyan 2 suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.