Isa ga babban shafi
Mozambique-Zimbabwe

Mutane dubu 600 na bukatar agajin gaggawa a Mozambique - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan 1 da dubu dari 7 annobar guguwar Idai ta shafa a kasar Mozambique, inda yanzu haka fiye da mutane dubu dari 6 ke tsananin bukatar agaji, dai dai lokacin da ake ci gaba da laluben mutanen da suka bace.

Rahotanni sun ce baya ga mutane da guguwar ta hallaka ta kuma yi awon gaba da tarin amfanin gona
Rahotanni sun ce baya ga mutane da guguwar ta hallaka ta kuma yi awon gaba da tarin amfanin gona REUTERS
Talla

Tuni dai gwamnatin Mozambique ta tabbatar da mutuwar fiye da mutane dubu guda a kakkarfar guguwar ta Idai wadda ta hadu da ruwan sama tare haifar da ambaliyar ruwan da ya kai ga rugujewar daruruwan gidaje baya ga bacewar fiye da mutane 200.

A safiyar yau Talata dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta fara isar da kayakin agajin abinci ga mutane fiye da dubu dari 6 da ke cikin tsananin bukatar agajin sakamakon yadda guguwar da ta hade da ambaliyar ruwa ta tagayyarasu.

Yanzu haka dai jamai’an agaji na ci gaba da laluben cikin baraguzan gine-gine don ceto wadanda ke da sauran lumfashi a kasar ta Mozambique da kuma wani bangare na Zimbabwe bayan shafe kwanaki 4 ana fuskantar guguwar ta Idai.

Kakakin hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Jens Laerke ya ce bannar guguwar ta wuce yadda mutane ke tunani, matakin da ya zama wajibi a gaggauta kai dauki ga mutanen da guguwar ta daidaita.

Ministan ci gaba muhalli na Zimbabwe, Joel Biggie ya ce ba kadai gidaje guguwar ta rusa ba, baya ga kisan tarin jama’a ta kuma yi awon gaba da tarin amfanin gonar yankunan da abin ya shafa wadanda ke gab da girbi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.