Isa ga babban shafi
Ethiopia

Ba wanda ya rayu a hadarin jirgin Ethiopia da ke hanyar zuwa Kenya

Rahotanni daga Addis Ababa na cewa ilahirin mutane 157 da ke cikin jirgin saman Ethiopian Airlines kirar Boeing 737 sun mutu a hadarin da jirgin ya yi da safiyar yau Lahadi.

Yanzu haka dai ana ci gaba bincike don gano cikakkun bayanan Fasinjojin da ke cikin jirgin kirar Boeing 737 don sanar da iyalansu
Yanzu haka dai ana ci gaba bincike don gano cikakkun bayanan Fasinjojin da ke cikin jirgin kirar Boeing 737 don sanar da iyalansu REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Jirgin wanda ya tashi daga Addis Ababa na kan hanyarsa ne ta zuwa Nairobi da safiyar Lahadi, dauke da fasinjoji 149 baya ga ma’aikatansa 8.

Ma’aikatar yada labaran kasar ta fitar da sanarwar cewa babu ko da mutun daya da ya tsira a jirgin wanda ya yi hadari jim kadan bayan tashin sa daga filin jirgin saman birnin na Addis Ababa.

Tuni dfai fadar gwamnatin kasar ta fitar da sanarwar gaggawa inda ta ke ruwaito shugaban kasar Abiy Ahmed na jajantawa wadanda ahalinsu ke cikin jirgin.

Yanzu haka dai ana ci gaba bincike don gano cikakkun bayanan Fasinjojin da ke cikin jirgin don sanar da iyalansu.

Jirgin kirar Boeing 737 irinsa ne dai da ya yi hadari a watan Oktoban bara mintuna 13 bayan tashinsa a birnin Jakarta na Indonesia tare da hallaka mutane 189.

Hadarin jirgin na yau a Ethiopia shi ne mafi muni na baya-bayan da ya afku bayan hadarin shekarar 2010 wanda shi ma dai jirgin ne kirar Boeing da ya taso daga Lebanon inda ya hallaka Fasinja 83 da ma’aikatan jirgi 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.