Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

INEC ta damkawa Buhari shaidar nasarar lashe zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da nasarar shugaban kasar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana ranar Asabar 23 ga watan nan, inda hukumar ta damka masa takardar shaidar nasarar lashe zaben. Wakilinmu Kabir Yusuf ya hada mana rahoto.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya ke karbar shaidar nasarar lashe zabensa karo na biyu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya ke karbar shaidar nasarar lashe zabensa karo na biyu RFI/ Bashir
Talla

Yayin wani kwarya-kwaryan biki da hukumar ta INEC ta jagoranta yau a Abuja, shugabanta Farfesa Mahmood Yakubu ya mika takaddar shaidar ga Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo wadanda za su jagoranci kasar a wa'adi na 2 na karin shekaru 4.

Yayin karbar shaidar cin nasarar, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ci gaba da bunkasa kasar daga yadda ya faro a shekarun hudun farko da ya shugabancin Najeriyar.

A cewar Ali Ndume guda cikin 'yan majalisun dattawan Najeriya akwai hasashen da ke nuna cewa, wa'adin na biyu zai samar da ci gaba fiye da na baya wanda ya yi da cin karo da matsaloli musamman a Majalisun kasar.

Ka zalika a cewarsa yanzu Najeriyar na gab da kara tono wasu ma'adanai wadanda ya ce za su taimaka matuka wajen samarwa kasar kudaden shiga don hidimtawa al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.