Isa ga babban shafi
Najeriya-Siyasa

Atiku ya fitar da sunan makusantan Buhari 28 da ya ke zargi da rashawa

Dan takarar shugabancin kasa a Najeriya Atiku Abubakar ya fitar da sunayen wasu mukarraban shugaban kasar Muhammadu Buhari ciki har da mai dakinsa Aisha Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a jerin wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa.

A cewar Atiku Abubakar kamata ya yi Buhari ya nemi yafiyar 'yan Najeriya kan kuncin da ya jefa na shekaru 4.
A cewar Atiku Abubakar kamata ya yi Buhari ya nemi yafiyar 'yan Najeriya kan kuncin da ya jefa na shekaru 4. AFP
Talla

Cikin sanarwar da kakakin Atiku Abubakar Phrank Shuaibu, ya fitar ga kafofin yada labaran kasar ya bukaci hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta INEC ta kwace rijistar da ta yi jam’iyya mai mulki ta APC yana mai cewa maimakon jam’iyyar siyasa ta juye zuwa matattarar cin hanci da rashawa.

Cikin zungureriyar sanarwar ta Atiku Abubakar wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriyar na tsawon shekaru 8, ya bayyana gwamnati mai mulki ta Muhammadu Buhari a matsayin mafi tagayyara kasar mai karfin tattalin arziki a Afrika.

Cikin mutane 28 da wasikar ta Atiku ta kunsa baya ga Aisha Buhari akwai kuma shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshimole da Abdullahi Adamu Dan Majalisar dattijai kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa sai kuma Folarin Coker babban daraktan hukumar yawon bude ido ta Najeriya akwai kuma Bola Tinubu.

Sauran sun hada Abba kyari da Babachir David Lawal sai Sanata Hadi Sirika da kuma Adedayo Thomas na hukumar Dab’I ta kasa baya ga Adamu Mua’azu tsohon gwamnan jihar Bauchi.

Haka zalika sanarwar ta fitar da sunayen Sen. Iyiola Omisore da Abdulrasheed Maina da kuma Sanata Musiliu Obanikoro wadanda dukkaninsu su ke da tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa amma gwamnatin Buhari ta rufa saboda kasancewarsu ‘yan Jam’iyyar APC.

Sauran sun hada da Orji Uzor Kalu da Issa Yuguda da Godswill Akpabio da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje baya ga Saminu Turaki tsohon gwamnan jihar Jigawa sai kuma Junaid Abdullahi da Aliyu Wamako na Sokoto kana da ‘yar takarar kujerar Gwamna a jihar Imo Hope Uzodimma.

Sanarwar ta karkare da sunayen Rotimi Amaechi da Abdul’ aziz Yari da kuma Maikanti Baru ka na da Ayodele Oke dukkaninsu mukarraban shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari.

A cewar sanarwar kamata ya yi Muhammadu Buhari ya nemi yafiyar ‘yan Najeriya kan cin amanarsu da ya yi tare da bayyana musu gaskiya game da yakinsa da cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.